Isa ga babban shafi
US- Philippine

Shugaban Philippine ya janye kalaman batunci ga Shugaban Amurka Obama

Shugaban kasar Amurka Barack Obama dake halartan taron kungiyar kasashen Kudu maso gabashin Asiya ya soke ganawa da shugaban Philippines Rodrigo Duterte, saboda abinda ake ganin kalaman batunci da aka yiwa Obama. 

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte
Shugaban Philippines Rodrigo Duterte REUTERS/Lean Daval Jr
Talla

Yanzu haka dai fadar Shugaban Philippines ta fitar da sanarwa inda take janye kalamun batunci da Shugaban na su yayi.

Da fari an shirya shugabannin biyu za su gana a wajen wannan taro da ake yi a Vietiane babban birnin Lao inda shugabannin kungiyar ke taron su na shekara-shekara  don karfafa dankon zumunci tsakanin su.

Sai dai kuma taron na bana babu armashi saboda sabanin dake tsakanin Amurka da Philippine, wadanda sun dade suna zumunci, kafin abin ya kaiga Shugaban Philippine na ta ruwan ashar kan Shugaban Amurkan dan tsakanin nan.

Jami'an Amurka sun bayyana cewa taron da aka shirya na shugaban kasashen biyu an soke saboda kalamai na baya-bayan nan da Shugaban Philippines ya rika yi cewa Obama dan karuwa ne.
Shugaban Philippine ya fadi cewa zai kara barota muddin Shugaban Amurkan ya nemi tursasa masa gameda kisan da ake yiwa masu muamulla da miyagun kwayoyi a Philippines.

A wannan shekara ne dai aka zabi Shugaba Rodrigo Duterte da kuri'u masu rinjaye, kuma ya zuwa yanzu mutane akalla 3,000 aka kashe saboda muamulla da miyagum kwayoyi, ma'ana tun hawansa shugabancin, duk rana akan kashe mutane akalla 44 ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.