Isa ga babban shafi
Philippines

Duterte na shan suka a Philippines

Ikirarin sabon shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte, na maido da hukuncin kisa ta hanyar rataya na ci gaba da samun suka daga cikin kasar, inda kungiyar mujami'ar Roman Katolika da ke kasar, wadda kashi 80 cikin 100 na al'ummar kasar ke bi, ta fito ta yi kakkausar suka game da kudirin shugaban.

Sabon shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Sabon shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte REUTERS/Rene Lumawag
Talla

Tun a jiya ne sabon shugaban ya yi ikirarin cewa daga ranar 30 ga watan gobe da zai  maido da hukuncin kisa tare da bai wa jami'an 'yan sanda izinin harbe duk wanda ya ki mika wuya bayan an zarge shi da aikata manyan laifuka.

Shekaru 16 kenan da aka jingine aiwatar da hukuncin kisa a kasar yayin da Mr. Duterte ke kokarin maido da shi.

Har ila yau, shugaban mai shekaru 71, ya yi alkawarin kafa dokar hana fita da misalin karfe biyu na dare domin kwankadon barasa a bainal jama’a, sannan kuma kuma zai hana kananan yara zirga zirga su kadai a cikin daren

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.