Isa ga babban shafi
Philippines

Duterte ya lashe zaben Philippines

Rahotanni daga kasar Philippines na cewa Rodrigo Duterte ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a jiya Litinin kamar yadda masu sa ido kan zaben suka sanar.

Sabon shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte
Sabon shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte REUTERS/Erik De Castro
Talla

Dan shekaru 71 Rodrigo Duterte ya lashe wannan zaben ne da babban rinjaye, inda ya samu kusan kashi 39 cikin 100, yayinda Mar Roxas ke bi ma sa da yawan kuriu sama da kashi 23, sai kuma Sanata Grace Poe da ta zo ta uku da yawan kuriu sama da kashi 21 cikin 100 na yawan kuriun da aka jefa.

Tuni dai Grace Poe wadda ta yi na uku ta taya sabon shugaban kasar murnar lashe zaben.

Shi dai sabon shugaban ya kasance mutun mai yawan soki burutsu idan yana jawabi, irin na Donald Trump na Amurka.

Koda a jawabinsa na ranar Asabar din da ta gabata a yayin rufe yakin neman zabe, sai da ya ce, da ya hau kan kujerar shugabancin kasar, to za a daina aikata laifuka cikin watanni shida a kasar.

Shugaban kasar mai barin gado Benigno Aquino ya gargadi mutanen kasar da su yi hattara domin kasar na iya fadawa cikin rikici.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.