Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa zata biya diyyar wadanda harin ta'addancin kasar ya rutsa da su

Gwamnati Kasar Faransa ta ce ta biya diyyar euro miliyan 85 ga iyalai da dangin mutane 130 da harin ta’addancin shekarar 2015 ya ritsa da su a birnin Paris. Yan ta’adda sun kaddamar da hari ne a filin wasan kwallon kafa, yayin da wasu Yan bindiga suka bude wuta a Bataclan da wurin cin abinci.

shagon Bataclan da aka kai harin ta'addanci
shagon Bataclan da aka kai harin ta'addanci REUTERS/Charles Platiau
Talla

Asusun dake kula da biyan diyyar ya ce mutane 2,625 suka gabatar da kan su kuma aka biya su diyyar Yan uwan su da dangin su da hare haren suka ritsa da su.

Julien Rencki, shugaban asusun biyan diyyar yace, ya zuwa yanzu yace daga cikin wadanda harin ya jikkata mutane 856 sun samu sauki daga raunuka daban daban da suka samu.

Jami’in yace suna saran biyan euro miliyan 300 ga wasu mutane 70 da suma suka gabatar da bukatar su, shekaru biyu da rabi bayan kai harin, idan an kamala tantance su.

A watan jiya, kotu ta daure wata mata watanni 6 a gidan yari, saboda tayi karyar cewar an harbe ta da bindiga lokacin kai harin.

Renki yace asusun na kuma shirin biyan akalla euro miliyan 200 zuwa 250 ga mutanen da harin ranar yanci ya ritsa da su a birnin Nice, a watan Yulin shekarar 2016, lokacin da wani dan ta’adda ya abkawa jama’a da motar sa, ya kuma kashe mutane 86.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.