Isa ga babban shafi
Faransa

An kama mutane 6 dake yunkurin kaiwa shugaban Faransa hari

Jami’an tsaron Faransa sun kama wasu mutane 6, bisa zarginsu da shirin kaiwa shugaban Faransa Emmanuel Macron hari.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. . Ludovic Marin
Talla

Majiyoyin tsaron Faransa sun ce an kame mutanen ne a wannan Talata bayan daukar lokaci ana sa ido kan harkokinsu, inda aka gano shirin da suke yi na farautar shugaban na Faransa.

Gidan talabijin na BFM dake Faransa, ya rawaito cewa, baki dayan mutanen 6, masu ra’ayi ne na rikau, ko da yake zargin bai tabbata ba a hukumance.

Wuraren da jamai’an ‘yan sanda suka kai samame yayin kamen sun hada da Isere dake kudu maso gabashin birnin Lyon, yankin Moselle dake iyaka da Jamus da Luxembourg, sai kuma arewacin birnin Rennes.

Lamarin dai ya zo ne kwanaki kalilan bayanda a ranar Lahadin da ta gabata, yayin zantawa da wasu manema labarai, shugaba Macron yayi gargadi kan hadarin karuwar masu rugumar “ra’ayin rikau”, ko na “mazan jiya”, abinda ya ce shi ne ya haifar da shugabanni irinsu Adolf Hitler na Jamus da Mussolini na Italiya, wadanda suka tada hankalin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.