Isa ga babban shafi
Faransa-ta'addanci

Faransa ta fara tuhumar mutanen da suka shirya kai wa musulmi hari

Bayan shafe kwana 4 a hannun yan sanda, a yau alhamis alkalin kotun hukunta laifukan taáddanci na Fransa ya tuhumi wasu mutane 10 da aka kama daga yankuna daban daban na kasar, bisa zargin alaka da wata Kungiyar da ke shirya kai hare-hare kan masalatai da kuma masu tsatsauran raáyin musulunci da aka sallama daga kurkuku a kasar ta Faransa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. LUDOVIC MARIN / POOL / AFP
Talla

Wadanda ake zargin sun hada da maza da mata da shekarunsu ya fara daga 32 zuwa 69 a garuruwa daban daban na kasar Faransa, bisa zarginsa da zama yan wata Kungiya da mahukunta ke zargi da zama mai hadarin gaske wajen tada fitina a cewar mai shigar da karar birnin paris.

Dukkanin mutanen 10 dai an gurfanar da su ne a gaban alkalin kotun hukunta laifukan taáddanci, inda majiyar sharia ta bayyana cewa, Wasu daga cikinsu an samesu da laifin mallakar makamai tare da kera ababe masu fashewa da ke da alaka da kungoyi yan taádda.

A lokacin da yan sanda suka kai samamen an yi nasarar kama bindigogi 36 da dubban harsasai, bayan haka kuma an gano cewa mutanen sun shiga kera ababe masu fashewa samfarin TATP.

Manufarta Kungiyar da ake kira Action des forces opérationnelles, AFO a takaice ita ce, yaki da masu tsatsauran raáyin musulunci a Faransa, Kungiyar da a halin yanzu ta bazu a cewar mai shigar da karar na birnin paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.