Isa ga babban shafi
Syria-Faransa

Faransa ta yi umarnin kame wasu jami'an leken asirin Syria

Kasar Faransa ta ba da sammaci ga kasashen duniya don kamo mata wasu jami’an leken asirin gwamnatin Syria guda 3 saboda zargin da ake musu na mutuwar wasu mutane biyu da ke zaune a kasar.

A cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Faransa FIDH mutanen biyu an kame su ne tun cikin watan Nuwamban shekarar 2013 ba kuma tare da wani dalili ba, ka zalika basa mara baya ga kungiyoyin da ke adawa da shugaba Bashar al-Assad.
A cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Faransa FIDH mutanen biyu an kame su ne tun cikin watan Nuwamban shekarar 2013 ba kuma tare da wani dalili ba, ka zalika basa mara baya ga kungiyoyin da ke adawa da shugaba Bashar al-Assad. REUTERS/Philippe Wojazer/Pool
Talla

Sammacin wanda ya shafi Daraktan liken asiri Ali Mamluk da wasu mutane biyu, zai bada damar tuhumar wadanda ake zargin da laifin azabtarwa da kuma kisa.

Sauran mutanen sun hada da Jamil Hassan, shugaban bangaren liken asirin sojin sama da Abdel Salam Mahmoud wanda shi ma ke aiki da sojin saman.

Dukkanin mutanen 3 Faransa na zarginsu da hannu a kisan Mazen Dabbagh mai shekaru 57 malami a wata makarantar Faransanci da ke birnin Damascus da kuma dansa Patrick Dabbagh mai shekaru 22 wanda dalibi ne a kasar ta Syria.

A cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Faransa FIDH mutanen biyu an kame su ne tun cikin watan Nuwamban shekarar 2013 ba kuma tare da wani dalili ba, ka zalika basa mara baya ga kungiyoyin da ke adawa da shugaba Bashar al-Assad.

Hukumar ta FIDH ta ce tun a ranar 8 ga watan Oktoba ne Faransa ta amince da mika bukatar kamen mutanen 3 amma ba a sanar da shi ga jama’a ba sai yau Litinin bayan tabbacin cewa mutanen biyu Faransawa sun mutu a hannun jami’an na Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.