Isa ga babban shafi
Faransa

ISIS ta dauki alhakin harin Marseille na Faransa

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin da wani mutum ya kaddamar da wuka a birnin  Marseille na Faransa, in da ya kahe mata 2 kafin daga bisani sojoji su samu nasarar harbe shi har lahira.

Hukumomin Faransa na gudanar da bincike kan harin wanda kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaddamarwa
Hukumomin Faransa na gudanar da bincike kan harin wanda kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaddamarwa Michel Euler / POOL / AFP
Talla

Wadanda lamarin ya auku a kan idonsu sun ce, maharin ya yi kabbara kafin ya yanke wuyar daya daga cikin matan.

Ministan cikin gidan Faransa Gerard Collomb ya ce, an yi wa akalla mutane 12 tambayoyi kan harin wanda ya ce ya yi kama da na ta’addanci.

Daga shekarar 2015 zuwa yanzu akalla mutane 239 aka kashe a hare-haren ta’addancin da aka kai a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.