Faransa za ta soma amfani da jiragen yaki a Sahel
Faransa ta bayyana shirin amfani da jiragen sama masu sarrafa kansu domin kai hare-hare kan ‘yan ta’addan da ke barazana a Yankin Sahel.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministan tsaron kasar Florence Parley ta ce shugaba Emmanuel Macron ya mayar da yaki da ‘yan ta’adda a matsayin babbar manufarsa na kasashen waje kuma dalilin haka ya sa aka dauki matakin.
Yanzu haka Faransa na da irin wadannan jirage guda 5 a birnin Yammai da ke Jamhuriyar Nijar domin taimakawa sojojinta 4,000 d ake yaki da ta’addanci a Afirka.
Faransa ta ce jiragen yakin za su kasance babbar barazana ga ‘yan ta’adda.
Manyan kasashe kamar Amurka da Birtaniya da Isra’ila na da jiragen yaki a kasashe da ke fama da rikici kamar Syria da Yemen da Iraqi da Afghanistan da kuma Somalia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu