Kaddamar da rundunar sojin Sahel sai da taimakon kasashen Duniya
Kasar Mali ta bukaci taimakon kasashen duniya wajen samun kudade da makamai domin kaddamar da rundunar sojin Sahel wadda za ta yi yaki da yan ta’adda dake ci gaba da kai munanan hare hare a Yankin.
Wallafawa ranar:
Jakadan Mali a Majalisar Dinkin Duniya Issa Konfourou, ya shaidawa kwamitin Sulhu cewar harin da aka kai Burkina Faso da ya hallaka mutane 18 da wanda aka kai Mali da ya kashe mutane 9 ya dada tababtar da muhimancin kaddamar da rundunar sojoji 5,000 da kasashen Nijar da Mali da Chadi da Mauritania da kuma Burkina Faso zasu bada gudumawar soji.
Ita dai wannan runduna na bukatar kudin da ya kai dala kusan miliyan 500 kafin fara aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu