Faransawa na zaben sabon shugaban kasa
Faransawa na gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu inda za su zabi sabon shugaba tsakanin ‘yan takara biyu Marine Le Pen da kuma Emmanuel Macron da ke fafatawa a zaben a yau Lahadi
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Zaben dai ya yi matukar daukar hankulan kasashen duniya, lura da irin bamabancin manufofi da ke tsakanin yan takarar biyu.
Sai dai an samu karancin rashin fitowar masu kada kuri’a a zaben na yau da ke dab da kammalawa cikin tsauraran matakan tsaro
Abdoulkarim Ibrahim Shikal da ke sa ido a zaben a Paris fadar gwamnatin kasar ya ce kashi 35 suka fito kada kuri’ar a zaben zagayen na biyu.
Zaben shugaban kasar zagaye na biyu da ake gudanarwa a Faransa ya fado ne a lokacin da Faransawa ke hutun karshen mako na kwanaki uku.
Wannan ne karon farko a shekaru 60 da ake gudanar da zaben zagaye na biyu ba tare da ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu ba.
Kuma a bana ana fafatawa ne tsakanin ‘yan takara Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayi da kuma Emmanuel Macron mai sassaucin ra’ayi.
Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka gudanar kafin zaben sun nuna cewa mutane 7 cikin 10 na masu kada kuri’a ba su da ra’ayin ‘yan takarar guda biyu
Muhimmacin zaben Faransa
Zaben dai nada matukar tasiri ga makomar Tarayyar Turai, lura da girman Faransa a matsayin ta biyu ga karfin tattalin arzikin nahiyar da kuma karfin soji da fada aji a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
Zaben kuma ana fafatawa ne tsakanin ‘yan takara da manufofinsu suka yi hannun riga da juna, wato tsakanin mai da’awar Tarayyar Turai da kuma mai adawa da kungiyar.
Samun nasarar Le Pen babbar baraka ce ga Tarayyar Turai musamman a daidai lokacin da Birtaniya ke shirin ficewa kungiyar da kuma sauyin da aka samu a Amurka na zaben Donald Trump, bako a siyayar duniya.
Ana dai sa ran samun sakamakon farko na zaben da misalin karfe 7 agogon GMT bayan kammala kada kuri’a.
A ranar 14 ga Mayu ake sa ran rantsar da duk wanda ya lashe zaben tsakanin Emmanuel Macron ko Marine Le Pen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu