Isa ga babban shafi
Faransa

Macron da Le Pen sun gudanar da zazzafar Mahawara

‘Yan Takaran shugabancin kasar Faransa Emmanuel Macron da Marine Le Pen sun gudanar da zazzafar mahawara a daren jiya Laraba, wadda ta mayar da hankali kan yaki da ta’addanci da tattalin arziki da kuma makomar kungiyar kasashen Turai.

Marine Le Pen da  Emmanuel Macron a lokacin tafka mahawara
Marine Le Pen da Emmanuel Macron a lokacin tafka mahawara REUTERS/Eric Feferberg/Pool
Talla

'Yan takaran biyu sun share dogon lokaci suna tafka muhawara da ya jan hankulan ‘yan kasar dama duniya, musamman ta yadda Le Pen ta danganta Macron da dan siyasa da ba shi da manufa ko alkibila.

Le Pen ta ce Macron dalibi ne da ke kokarin wanke kan sa daga wasu laifukan Gwamnatin Shugaba Hollande.

A lokacin da ya ke mayar mata da martani Emmanuel Macron ya kawo hujojjin da suka sha baban da tsarin Le Pen, kuma ya danganta ta, da ‘yar takara da ke kokarin zura Faransa cikin wani yanayi na kaka ni ka yi.

Macron ya kuma kara da cewa Le Pen ''karya ta ke'', a kan wasu daga cikin tsare-tsaren da ta sanar, saboda haka ta fadawa ‘yan kasar gaskiya.

Wasu daga cikin alkaluman farko daga masu lura da siyasar Faransa sun bayyana cewa Macron ya taka gaggarumar rawa a wannan muharawa inda kusan kashi 63 na ‘yan kasar suka yi na'am da amsoshin da ya bayar.

Kana kashi 34 cikin 100 na Faransawa suka yi na'am da amsoshin ‘yar takara Marine Le Pen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.