Le Pen ta kwafi jawabin Fillon
An zargi ‘Yar takarar shugabancin Faransa Marine Le Pen da satar jawabin Francois Fillon na Jam’iyyar Republican da ya sha kaye a zagaye na farko a wani jawabin da ta gabatar a ranar Litinin a Paris.
Wallafawa ranar:
Le Pen ta gabatar da jawabinta kamar na Fillon ba tare da sauya kalma ba.
A ranar 15 ga watan Afrilu ne, Fillon ya bayyana a cikin jawabin da ya gabatar a Puy-en-Velay cewa Fransa nada iyaka ta tsaunukan da suka hada ta da kasar Italiya ‘yan uwa, da wani gefen kasar Sifaniya kai har zuwa Turai ta tsakiya da balkan da kuma yammacin Turai.
Amma Kwanaki 15 bayan gabatar da wannan jawabi, na Fillon, a lokacin da ta ke jawabi a gaban magoya bayanta a Villepinte a Seine-Saint-Denis, Le Pen, a kokarinta na son birge magoya bayanta ta maimaita kalmomin da Fillon ya yi amfani da su a jawabinta.
A ranar Lahadi ne Le Pen za ta fafata da Emmanuel Macron a zaben shugaban kasa zagaye na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu