Isa ga babban shafi
Faransa

Le Pen ta sauya tunani a kan EU

Sakamakon kulla kawance da daya daga cikin ‘yan takarar da suka sha kaye a zagayen farko na zaben shugabancin kasar mai suna Nicolas Dupont-Aignan, Marine Le Pen, ta ce ta jingine batun kiran zaben raba gardama domin ficewa daga Turai.

Marine Le Pen da ke takara a Jam'iyyar Front national ta Faransa
Marine Le Pen da ke takara a Jam'iyyar Front national ta Faransa REUTERS/Jean-Pierre Amet
Talla

Le Pen ‘yar takarar jam’iyyar masu zazzafen ra’ayin kishin kasa, da ke ci gaba da fuskantar Suka daga Shugaba Faransa mai ci Francois Hollande, ta ce a cikin watanni shida idan ta samu nasara a zaben kasar zata bari har sai an gudanar da taron ‘yan Majalisar Turai a shekara ta 2018,kafin ta waiwaye batun fidda Faransa daga EU.

Masu lura da lamurran siyasar kasar ta Faransa dai na kallon matakin a matsayin wanda ya yi hannun riga da alkawurkan da ‘yar takarar ta daukar wa Faransawa a baya.

A wani labarin kuma Jean-Luc Melenchon wanda ake kallo a matsayin dan takarar masu ra’ayin kominisanci, wanda kuma ya samu sama da 19,6% na kuri’un da aka kada a zagayen farko na zaben Fransa, ya ce zai kasance babban kuskure idan aka zabi Marine Le Pen domin shugabancin kasar a ranar lahadi mai zuwa.

Melenchon wanda ke zantawa da tashar talabijin ta TF1 , ya ki yin kira ga magoya bayansa da su jefa wa wani dan takara a zaben na jibi, to sai dai ya bukaci daya dan takarar Emmanuel Macron da ya yi sassauci a cikin wasu daga cikin manufofinsa na siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.