Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawa ke da Ikon zabin kasancewa a EU-Hollande

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce ci gaba da kasancewar kasar cikin Kungiyar Tarayyar Turai wato EU na hannu ‘yan kasar da zasu kada kuri’ar zabe a ranar 7 ga watan mayu.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Christophe Petit Tesson/Pool
Talla

Hollande ya Ambato haka ne tare da sake jadada goyon bayansa ga Emmanuel Macron da kuma nuna adawarsa ga Maria Le Pen da ke da manufar fidda kasar daga EU.

Hollande da ke jawabin karshe a matsayinsa na Shugaban Faransa a Taron EU, ya ce Faransawa kawai ke da daman hana fidda kasar daga EU, kuma barin kungiyar ba zai haifar da ci gaba ba face wahala.

Jawaban shugaban na zuwa ne bayan Le Pen ta sanar cewa za ta Nada Nicolas Dupont-Aignan wanda ba ya ra’ayin EU a matsayin Frimiya kasar idan ta yi nasara a zaben na mako mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.