Isa ga babban shafi
Faransa

An samu sauyi a siyasar Faransa

Emmanuel Macron da Marine Le Pen ne za su je zagaye na biyu na zaben shugabancin Faransa wanda za a yi nan da kwanaki 13 masu zuwa, bayan nasarar da suka yi a zagayen farko da aka gudanar a ranar Lahadi.

Emmanuel Macron da Marine Le Pen 'Yan takarar da za su fafata a zagaye na biyu a zaben Faransa
Emmanuel Macron da Marine Le Pen 'Yan takarar da za su fafata a zagaye na biyu a zaben Faransa JEFF PACHOUD / AFP
Talla

Macron wanda ba ya da jam’iyyar siyasa illa kawai gungun aminai da ke mara ma sa baya, ya samu kashi 24,01, yayin da Marine Le Pen ‘yar takarar ma su zazzafen ra’ayin kishin kasa ta samu 21,30.

Fitar da wannan sakamakon dai ya zo wa wasu Faransawa ba-zata, musamman wadanda ke mara wa François Fillon dan takarar babbar jam’iyyar adawa, yayin da daya dan takarar mai suna Jean Luc Mélenchon da ake kallo a matsayin mai ra’ayin kominisance ya nuna shakkunsa ga sakamakon.

Macron wanda bako ne a fagen siyasa duk da cewa ya taba rike mukamin ministan tattalin arziki a karkashin gwamnati mai ci, to amma ya samu nasarar ne sakamakon yadda ya dauki matakin raba gari da wadanda suka fito da shi a fagen siyasa.

RFI

Wannan dai yana nufin cewa wanda ba ya da jam’iyyar siyasa ya yi nasarar zuwa zagaye na biyu a zaben kasar a cikin shekaru masu tarin yawa, lamarin da kuma masu manazarta ke dangantawa da yadda aka kosa da siyasa ko kuma kamun lodayin jam’iyyun da suka mamaye salon siyasar Faransa.

Farin jinin Jam’iyyar ‘Yan kishin kasa

Abin fargaba ga wasu Faransawa da kuma sauran ‘yan siyasa a yankin Turai shi ne yadda Marine Le Pen ‘yar takarar masu zazzafen ra’ayin kishin kasa ta samu kashi sama da kashi 21 cikin dari na kuri’un da aka jefa.

Duk da ra’ayinta na kyamar baki da kyamar addinin Islama, da kuma ikirarinta na ftar da Faransa daga Turai, Le Pen ta samu kuri’u milyan 7 da dubu 700 a zagayen farko, kuma tabbas ta kara farin jini ne idan aka kwantanta da kuri’un da ta sama a zaben shekara ta 2012.

Faduwar manyan Jam’iyyu

Wannan zabe ne da ya kara fito da matsayin jam’iyyun da suka saba mulkin Faransa wato Socialist da kuma Les Republicains tsohuwar UMP, duka duka ‘yan takararsun, Benoit Hamon da François Fillon sun samu kashi 26 na kuri’un da aka jefa a zagaye na farko baki daya.

Ma’ana dai ba daya daga cikinsu da zai je zagaye na biyu na wannan zabe.
Benoit Hamon dan takarar jam’iyyar mai mulki ya samu kashi 6.3% ne, abin da wasu ke fassarawa a matsayin tozartarwa ga jam’iyyar da ta share shekaru 5 tana mulki.
Shi kuwa François Fillon, duk da cewa ya samu 19.9%, amma dai ba zai je zagaye na biyu ba.

Macron ya samu goyon bayan Turai

Kasashen duniya da dama ne suka aike wa Emmanuel Macron sakon taya murna saboda wannan nasara ta zuwa zagaye na biyu da ya samu, cikinsu har da shugabar gwamanatin Jamus Angela Merkel, da shugaban Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce zai jefa wa Macron kuri’a a zagaye na biyu na zaben mai zuwa, inda ya bayyana zaben Le Pen a matsayin wanda zabenta ke tattare da matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.