Isa ga babban shafi
Faransa

'Yar Takaran Shugabancin Faransa Le Pen ta Sanar da Mutumin da za ta nada Firaminista

‘Yar takaran shugaban kasar Faransa mai kishin kasa Marine Le Pen ta sanar da cewa muddin ta yi nasarar zaben dake tafe to kuwa abokin takaranta da ya sha kaye a zagaye na farko Nicolas Dupont-Aignan za ta nadashi Firaminista.

Nicolas Dupont-Aignan tare da  Marine Le Pen  a wani hoto da aka dauka a Paris ranar Juma'a 29 aprilu  2017.
Nicolas Dupont-Aignan tare da Marine Le Pen a wani hoto da aka dauka a Paris ranar Juma'a 29 aprilu 2017. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Shi dai Nicolas Dupont-Aignan ya sami yawan kuriu kashi 4.7%  a zabe zagaye na farko da aka yi ranar 23 ga wannan wata mai karewa.

Ya sanar bayan wancan zabe cewa yana goyon bayan uwargida Marine Le Pen a zaben da zata fafata da Emmanuel Macron a zagaye na biyu ranar 7 ga watan  Mayu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.