Isa ga babban shafi
Faransa

Goyan baya zuwa yan takarar zaben Faransa

Daya daga cikin yan takara a zaben Shugabancin kasar Faransa Nicolas Dupont Aignan ya sanar da bada goyan bayan sa zuwa yar takara Marine le Pen a zagaye na biyu.Zinedine Zidane a na sa bangaren ya kira faransawa zuwa ga zaben Emmanuel Macron a zagaye na biyu. 

Marine Le Pen da Emmanuel Macron  a Faransa
Marine Le Pen da Emmanuel Macron a Faransa REUTERS/Eric Gaillard
Talla

A daya wajen ,wakilan kafofin yada labarai sama da 30 dake kasar Faransa sun gabatar da koken su inda suke zargin jamiyyar ‘yar takaran shugabancin kasar Marine Le Pen da hana su yin kusa da ita don samun labarai.

A cewar su Jamiyyar Marine Le Pen ke zaben irin kafafen yada labarai da suke bukata su dauki labaran su al’amari daya sa kafofin yada labarai da yawa gaza sanin halin da Jamiyyar ta National Front ke ciki.

Cikin manyan kafofin yada labarai da wakilansu suka sanya hannu cikin takardan koken akwai na Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP, da Jaridar Le Monde da jaridar Le Figaro da tashoshin Talabijin na TF1 da BMF da Channels da kuma Tashan Radio France Info.

Takardar koken na nuna matukar bacin rai yadda Jamiyyar ke hana ‘yan jaridu gudanar da aikin su a wannan lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.