Isa ga babban shafi
Faransa

Tarihin Marine Le Pen da ke takara a Faransa

An haifi Marine Le Pen a ranar biyar ga watan Augusta a shekarar 1968, kwararriyar lauya ce, kuma ita ce shugabar jam’iyyar National Front mai kishin kasa.

Uwargida Marine Le Pen ta jam'iyyar National Front mai ra'ayin kishin kasa
Uwargida Marine Le Pen ta jam'iyyar National Front mai ra'ayin kishin kasa REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Marine Le pen ‘ya ce ga shahararren dan siyasar Faransa Jean-Marie Le Pen.

Le Pen dai ta rike mukamin kansila tun daga shekarar 1998, sannan mamba ce a Majalisar Dokokin Turai tun daga shekarar 2004 har ya zuwa yau.

A shekarar 2011 ne ta zama shugabar jam’iyyar National Front bayan ta lashe zaben da aka gudanar da kashi kusan 68 cikin 100 bayan sun fafata da abokin hamayyarta Bruno Gollnisch. Hakan ya sa ta maye gurbin mahaifinta da ya shugabancin jam’iyyar tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1972.

A shekarar 2012, Marine Le Pen ta zo ta uku a zaben shugabancin kasar da kashi 17. 90 na kuri’un da aka kada, wannan dai shi ne karo na biyu da Le Pen ke sake nuna sha’awar zama shugabar kasar Faransa.

Rikici dai ya taba barkewa tsakanin Marine Le Pen da mahaifinta Jean Le Pen kan sabanin ra’ayin tafiyar da jam’iyya, al’amarin da ya kai har ta kori mahafin daga zama mamba a jam’iyyar ta National Front.

Marine Le Pen ta na da matsanancin ra'ayin rikau da kuma adawa da 'yan gudun hijira, ga kuma nuna kyama ga wasu al’addu na musulunci da ta ce, sun yi hannun riga da al’addar Faransawa.

Uwargida Marine Le Pen na da ‘ya’ya uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.