Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan takara a zaben Faransa na tarukan gangami a wannan litinin

Yayin da ya rage kwanaki 6 a gudanar da zaben shugaban kasar Faransa, a wannan litinin biyu daga cikin manyan ‘yan takara a zaben Marine Le Pen ta jam’iyyar masu ra’ayin rikau da Emmanuel Macron da ke bayyana kansa a matsayin mai tsaka-tsakan ra’ayin na gudanar da tarukan gangami a birnin Paris.

Gangamin Jean-Luc Mélenchon a Toulouse 16-04-2017.
Gangamin Jean-Luc Mélenchon a Toulouse 16-04-2017. REUTERS/Regis Duvignau
Talla

Shi kuwa Francois Fillon na babbar jam’iyyar adawa na gudanar da taron gangami ne a garin Nice yayin da Jean-Luc Melenchon da ake dangatawa da masu ra’ayin kwaminisanci ke shirin gabatar da jawabi ga magoya bayansa a birnin Paris a wannan litinin.

‘Yan takara 11 ne ke shirin fafatawa da juna a zaben da za a yi ranar 23 ga wannan wata, kuma 7 daga cikinsu sun taba tsayawa takara a zabukan da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.