Isa ga babban shafi
Faransa

Manufofin 'yan takarar Faransa kan samar da aiki

Daya daga cikin manyan batutuwan da masu zabe a Faransa suka fi maida hankali a kai shi ne batun samar da ayyukan yi a kasar, idan aka yi la’akari da sakamakon wani bincike da hukumar kidddidigar kasar ta fitar, da ya nuna cewa cikin matasa hudu ‘yan kasa da shekaru 25 , guda ba shi da da aikin yi.

'Yan takara 11 ne ke neman kujerar shugabancin Faransa a bana
'Yan takara 11 ne ke neman kujerar shugabancin Faransa a bana REUTERS/Eric Gaillard/File Photo
Talla

Kididdigar ta nuna cewa kasar Faransa ita ke a matsayi na 8 daga cikin jerin kasashen Tarayyar Tturai da tafi fama da matsalar ayyukan yi.

Kazalika wani bincike da aka gudanar a farkon watan da muke ciki ya nuna cewa kashi 55 cikin 100 na al’ummar Faransa sun bayyana cewa, manufar dan takara kan warware matsalar aikin yi, ita ce za ta taka rawa wajen yanke shawarar wanda za su kada wa kuri’a a zaben da za gudanar da zagayen farko a ranar 23 ga watan Afrilu da muke ciki.

Idan muka fara da manufar dan takara mai zaman kansa Emmanuel Macron, ya ce daga cikin bajintar da zai nuna wa Faransawa idan suka ba shi ragamar jan kasar a hannunsa, musamman kan batun tattalin arziki da ya shafi samar da ayyukan yi, shi ne tara wa kasar Euro biliyan 60 cikin shekaru biyar tare da zuba Euro biliyan 50 a baitil-malin kasar don bunkasa tattalin arziki.

Kazalika Macron ya ce, zai rage yawan ma’aikatan gwamnatin kasar dubu 120,000 don samun damar rage yawan harajin da aka sanya wa kamfanoni da gidajen haya da Euro biliyan 20 don fadada damar ayyukan yi da kamfanonin ke samarwa.

Ana ta bangaren kuwa kan batun samar da aiki, ‘yar takarar shugabancin Faransa mai kishin kasa Marine Le Pen cewa ta yi, za ta tsaurara biyan haraji ne ga ma’aikatan da suka kasance ba ‘yan kasa ba don rage yawan wadanda ke tururuwa kasar don samun aikin yi, wanda ta ce ko shakkah babu hakan zai rage matsalar rashin aikin yi tsakanin Faransawa.

Francois Fillon na jam’iyyar adawa ta Republican, alwashi ya sha na rage yawan wadanda ba su da ayyukan yi a kasar zuwa kashi 7 daga kashi 10 da ake da shi a yanzu.
 

Ya ce zai kara wa’adin shekarun ajiye aiki da rage yawan kudaden alawus da ake bai wa ma’aikata a kasar, sai kuma rage yawan ma’aikatan gwamnati akalla dubu 500,000 don amfani da kudaden wajen bunkasa kamfanoni a kasar abin da wasu ke cewa abin azimun ne wai jifan sauro da gatari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.