Isa ga babban shafi
Faransa

Takaitaccen tarihin Francois Fillon dan takara a zaben Faransa

A ci gaba da gabatar ma ku da takaitaccen tarihin ‘yan takarar neman shugabancin kasar Faransa a zaben da za a yi a ranar lahadi mai zuwa, a yau za mu gabatar ma ku da tarihin siyasar Francois Fillon ne, wato dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta Republican, daya daga cikin mutane 11 da za su fafata da juna a zaben na ranar 23 ga wannan wata.

François Fillon na zantawa da RFI ranar 6-04- 2017.
François Fillon na zantawa da RFI ranar 6-04- 2017. RFI/Romain Ferre
Talla

François Charles Amand Fillon mai shekaru 63 a duniya, an haife shi ne a garin Le Mans da ke jihar Sarthe a Faransa, kuma ya fara siyasa ne tun yana dan shekaru 23 a duniya. Sunan mahaifinsa Fillon wanda lauye ne sai kuma mahaifiyarsa mai suna Anne Soulet malamar tarihi.

Ya samu digrinsa na farko ne a fannin shari’a a 1976, to amma bai tsaya a nan ba domin ya ci gaba da karatu har zuwa lokacin da ya samu digiri na biyu domin gogewa a fannin sannin dokoki a jami’ar Paris Descastes.

Francois Fillon ya goge sosai a fagen siyasa, ta hanyar rike mukamai da dama da suka hada da ministan kare muhalli, na sufuri da kuma gina gidaje, kafin nan ya rike wasu mukamai da suka hada da ministan ilimi, na kwadago, sadarwa da dai sauransu, kafin a ba shi mukamin Firaminisya wanda ya rike daga 2007 zuwa 2012 lokacin mulkin Nicolas Sarkozy.

Fillon wanda ke tsaya wa jam’iyyar Les Republicains wato tsohuwar jam’iyyar UMPt akara, yana da mata mai suna Penelope Clarke, kuma yana da ‘yaya 5. Ya yi nasarar kasancewar dan takarar jam’iyyar ne a cikin watan nuwambar bara sakamakon doke tsohon Firaministan Alain Juppe a zagaye na biyu a zaben fidda gwani, amma kafin nan ya doke wasu ‘yan takarar cikin har da tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.