Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdogan ya kwatanta gwamnatin Merkel da ta ‘yan Nazi

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya soki gwamnatin Jamus bayan haramta wa ‘yan Turkiya gudanar gangami a kasar kan shirin kada kuri’ar jin ra’ayi game da kara masa karfin iko. Cikin martaninsa, Erdogan ya bayyana matakin na Jamus da cewa ba shi da banbanci da na gwamnatin Nazi a kasar da ta shude.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan AFP
Talla

Kalaman na Erdogan na zuwa kwana guda bayan da ya zargi gwamnatin Jamus da taimakawa ayyukan ta’addanci, ta hanyar kyale jagororin jam’iyyar kurdawa da ta dauka a matsayin ‘yan ta’adda gudanar da tarukansu a Jamus.

Hukumomin biranen Jamus da dama ne suka haramtawa ministocin gwamnatin Erdogan jagorantar gudanar da manyan taruka, tare da kare matakin da cewa sun yi hakan ne bisa dalilai na tsaro.

Turkiya ta bukaci Karin bayani daga jakadan jamus a kasar kan yadda Jamus din ta hana ministan Shari’ar Bekir Bozdag, gabatar da jawabin goyon bayan karawa Erdogan karfin zama shugaban kasa mai cikakken iko.

Sai dai kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta yi watsi da zargin na Turkiya tare da cewa gwamnatocin kananan hukumomin kasar sun hana gangamin ne don tabbatar da doka amma ba don tauyewa kowa damar bayyana ra’ayi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.