Majalisar Turkiya ta amince da karawa Erdogan karfin iko
Majalisar kasar Turkiya ta goyi bayan wani kuduri da zai karawa shugaban kasar Recep Tayyib Erdogan karfin iko.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kudurin ya samu goyon bayan ‘yan majalisu 339 yayinda 142 suka kada kuri’ar adawa da kudurin.
Idan har kudurin ya samu amincewar al’ummar kasar ta Turkiya a kuri’ar jin ra’ayi da zasu kada, a karo na farko za’a samar da shugaba mai cikakken iko a kasar tare da soke mukamin Firaminista a karo na farko a tarihin Turkiya.
Zalika karkashin kudurin za’a rika gudanar da zaben Majalisar kasar da na shugaban kasa a lokaci guda, wanda ake sa ran tsaida ranar 3 ga watan Nuwamban 2019 a matsayin ranar gudanar da zaben.
Ana sa ran kada kuria’ar jin ra’ayin jama’ar a watan Afrilu mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu