Isa ga babban shafi
Turkiyya

Turkiyya ta kore dubban Ma'aikata

Hukumomi a kasar Turkiyya sun kori ma'aikata samada dubu shida da haramtawa wasu kungiyoyi da dama aiki a fadin kasar a wani sabon matakin tankade da rairaya, bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba bara.

Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan bayan wata ziyara a kasar Masar.
Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan bayan wata ziyara a kasar Masar. REUTERS/Huseyin Aldemir
Talla

Matakin na karkashin tsarin dokar ta baci da hukumomin kasar ke aiwatarwa tun bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Tuni dai an dauki matakan dakatarwa da koran  mutane sama da dubu daya daga ayyukan Gwamnati saboda muamulla da wadanda ake zargi da hannu wajen yunkurin kifarda Gwamnati.

Wata sabuwar doka da Gwamnatin ta fitar na cewa an kori ‘yan sanda 2,687 bayaga wasu dimbin fararen hula da aka sallama daga aiki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.