Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta musanta ikirarin IS na kona sojinta

Gwamnatin Turkiyya ta ce babu tabbacin hoton bidiyon da mayakan IS suka fitar na kona sojin kasar biyu da ransu gaskiya ne. 

Hoton bidiyon da IS ta nuna, in da ta kona sojin da ta ce na Turkiya ne bayan ta kama su a Syria
Hoton bidiyon da IS ta nuna, in da ta kona sojin da ta ce na Turkiya ne bayan ta kama su a Syria mirror.co.uk
Talla

Mataimakin Firaministan Turkiyya Numan Kurtulmus ya ce, babu wata hujja da ke tabbatar da cewar sojin kasar ne a hoton bidiyon da mayakan suka yada a shafinsu na intanet.

Kurtulmus ya kara da cewa, babu bayani daga dakarun kasar da ke Syria ko ma’aikatar tsaron Turkiyya da ke tabbatar da hakan.

Mataimakin Firaministan ya yi bayanin ne a kafar yada labaran gwamnatin kasar, in da ya kuma ce, in har an tabbatar da gaskiyar al’amarin, to za a sanar da jama’a.

Bayyana hoton bidiyon da ke nuna mayakan IS na kona sojojin na Turkiya da ransu ya matukar tayar da hankulan jama’ar kasar.

Watanni hudu kenan da dakarun sojin Turkiya suka shiga Syria, in da suke fafatawa da mayakan IS da zimmar taimaka wa dakarun gwamnati don sake kwace garin Al Bab da ya fada hannun kungiyar a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.