Isa ga babban shafi
Turkiya

An gano maharin gidan rawar Turkiya

Hukumomin Turkiya sun gano maharin da ya kashe mutane 39 da ke cashewar murnar sabuwar shekara a gidan rawar Reina da ke birnin Santanbul.

Jami'an 'Yan Sandan Turkiya na farautar maharin Santanbul
Jami'an 'Yan Sandan Turkiya na farautar maharin Santanbul
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Mevlut Cavusoglu ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Anadolu cewa, an tantance hakikanin maharin da kungiyar IS ta ce mayakinta ne.

To sai dai ministan bai bada suna da kuma cikakkun bayanai game da maharin ba, wanda ya harba arsashai 120 kan jama’ar da ke cashewar a ranar Lahadi.

Kafofin yada labaran Turkiya sun rawaito cewa, maharin ya yi hayar wani gida a birnin Konya kafin daga bisani ya isa Santanbul don kaddamar da wannan farmakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.