Turkiya na farautar dan bindigar da ya kashe mutane 39
‘Yan sandan Turkiya na farautar wani Dan bindiga da ya kashe mutane 39 yawancinsu ‘yan kasashen waje a harin da ya kai a wani gidan cashewa a Istanbul a jiya Lahadi.
Wallafawa ranar:
Dan bindigar ya bude wuta ne kan mai uwa da wabi lokacin da mutane ke cashewar murnar sabuwar shekara a Istanbul.
Turkiya ta alakanta maharin da kungiyar IS da ta ke zargin ya fito ne daga tsakiyar yankin Asia.
Tun a farkon Disamba Jami’an tsaron Turkiya suka kaddamar da farautar ‘Yan ta’adda bayan samun bayanai akan yiyuwar kai hare hare a lokacin bukukuwan sabuwar shekara a biranen kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu