Jamus ta shashantar da kiran jakadanta a Turkiya
Gwamnatin Jamus ta shashantar da matakin da Turkiya ta dauka na kiran jakadanta bayan gangamin da magoya bayan shugaba Erdogan suka yi a birnin Cologne .
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun ministan harkokin wajen Jamus, Martin Schaefer ya ce, kiran jakadanta da Turkiya ta yi ba wani muhimmin abu bane, lura da cewa an saba ganin haka tsakanin kasashe biyu da ke huldar diflomasiya.
Sai dai Schaefer ya tabbatar wa manema labarai cewa, kiran nada nasaba da gangamin da magobayan Erdowan din suka yi a jiya.
An dai gudanar da gangamin ne don nuna goyon baya ga Erdogan saboda yunkrin juyin mulkin da aka yi masa a ranar 15 ga watan jiya duk da cewa juyin mulkin bai yi nasara ba.
Kimanin Turkawa miliyan uku ne ke zaune a Jamus, kuma ita ce kasar waje da Turkawan suka fi yawa a ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu