Isa ga babban shafi
Turkey

Kasar Turkiyya ta saki sama da sojoji 750

Kasar Turkiyya ta saki sama da sojoji 750 daga tsare su da ta yi wadanda aka kama bayan yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasar Racep Tayyib Erdogan. 

Turkiya ta saki sojoji 750 daga kurkuku
Turkiya ta saki sojoji 750 daga kurkuku Reuters/Stringer
Talla

Matakin ya zo ne bayan da Erdogan ya bayyana cewa zai janye matakin gurfanar da wadanda suka ci zarafinsa, a wani yunkuri na sake karfafa hadin kan yan kasar ta Turkiyya.

Sama da yan kasar 60,000 ne suka fuskanci tsarewa a gidan yari, kora daga aiki, ko kuma dakatarwa, saboda zarginsu da ake da hannu cikin yunkurin juyin mulkin da bayi nasara ba a kasar.

Kasashen turai dai sun soki yunkurin juyin mulkin wanda gwamnatin Turkiyyan ta ce mutane 237 ne suka rasa rayukansu, yayin da kuma 2,100 suka samu raunuka.
Sai dai kuma nahiyar turan ta bayyana damuwa bisa yawan mutane da Turkiyyan da garkame ko kora daga aiki saboda zarginsu da ake da hannu cikin yunkurin juyin mulkin.

Sai dai a bangarensa Shugaban Turkiyyan ya bukaci kasashen yamman dake sukar matakan da gwamnatinsa ke dauka su daina yi masa katsalandan.

Kawo yanzu a ana tsare da yan jarida 17 wadanda ake tuhumar suna da alaka da barazana ga tsaro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.