Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya za ta rusa rundunar tsaron fadar gwamnati

Gwamnatin Turkiya za ta rusa rundunar da ke da alhakin tsaron fadar shugaban kasa bayan kame kusan 300 daga cikin dogarawan rundunar sakamakon yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ba a kasar.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan na ci gaba da daukan tsauraran matakai kan wadanda ake zargi da kokarin kifar da gwamnatinsa
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan na ci gaba da daukan tsauraran matakai kan wadanda ake zargi da kokarin kifar da gwamnatinsa Reprodução
Talla

A wata hira da aka yi da shi a kafar tababijin din kasar, Firaministan Turkiya, Binali Yildrim ya bayyana cewa yanzu haka, ba a bukatar rundunar baki daya.

Tun bayan yunkurin juyin mulkin ne, shugaban kasar Recep Tayip Erdogan ke ci gaba da daukan tsauraran matakai kan wadanda ake zargi da kitsa kifar da gwamnatinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.