Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta cafke yaron Gulen

Mahukuntan Turkiya sun cafke wani da ga malamin kasar Fethullah Gulen da ke zama a Amurka wanda ake zargi da kitsa juyin mulkin da aka murkushe. An cafke Muhammad Sait Gulen a Erzurum gabashin Turkiya kuma an tafi da shi zuwa Ankara fadar gwamnatin kasar.

Turkiya na zargin Fethullah Gülen da jagorantar juyin mulkin da aka murkushe
Turkiya na zargin Fethullah Gülen da jagorantar juyin mulkin da aka murkushe AFP/SELAHATTIN SEVI / ZAMAN DAILY
Talla

Yanzu haka kuma gwamnatin Raccep Tayyip Erdogan ta tsawaita dokar, lokacin da za a ci gaba da tsare mutun har zuwa kwanaki 30 ba tare da hukunci ba tare da rufe makarantu sama da 1000.

Sama da mutane dubu 66 aka cafke wadanda ake zargi suna da hannu a yunkurin juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.