Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta sanar da sabbin matakan tasa keyar miliyoyin baki

Ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka ta sanar da sabbin matakai da take shirin dauka domin gaggawar kwashe milyoyin baki da ke zauna a kasar ba tare da mallakar takardun izinin zama ba.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Bincike ya nuna cewa sama da mutane miliyan 11 ne aka tabbatar da cewa suna zaune a Amurka, ba tare da mallakar takardun izinin yin hakan ba, kuma sabbin matakan da za’a dauka za su shafe su matukar aka aiwatar da su.

A matakin farko sakataren tsaron cikin gida John Kelly, ya bai wa jami’an shige da fice da kuma hukumar kwastam izinin gaggauta tasa keyar marasa takardu da ke zaune a kasar.

An karkasa bakin hauren zuwa gida 7, na farko da za’a kwashe, su ne wadanda aka samu da aikata laifuka a Amurka, da wadanda ake zargi da aikata laifukan, kafin kotu ta tabbatar da hakan.

Zalika matakin zai rusa wata doka da tsohon shugaban kasar Barack Obama ya dauka a shekara ta 2012, wadda ke bai wa marasa takardu damar zama a Amurka.

Sakataren tsaron cikin gidan kasar, zai yi amfani da kudurin doka da Donald Trump ya sanya wa hannu ranar 25 ga watan Janairun da ya gabata, wanda a karkashinsa shugaban ke cewa zai gina katanga tsakanin Amurka da Mexico.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.