Isa ga babban shafi
Amurka

Mai bai wa Trump Shawara kan tsaro ya yi murabus

Mai Bai wa shugaban Kasar Amurka Donald Trump shawara kan harkokin tsaro Michael Flynn da ake zargi da tattaunawa da Jakadan Rasha kan cirewa kasar takunkumi ya sauka daga mukamin sa.

Mai bai wa Trump shawara kan tsaro Michael Flynn ya yi Murabus
Mai bai wa Trump shawara kan tsaro Michael Flynn ya yi Murabus REUTERS/Carlos Barria
Talla

Flynn ya musanta zargin da ake masa, abinda ya sa mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya fito fili ya bayyana goyan bayan sa a bainar jama’a.

A wasikar da ya rubuta na sauka daga mukamin sa, Flynn wanda tsohon jami’in leken asirin rundunar sojin Amurka ne, ya nemi gafarar shugaba Trump da mataimakin sa kuma ya ce sun amince.

Fadar shugaban ta ce Trump ya amince da nadin Janar Joseph Kellogg a matsayin wanda zai rike kujerar na wucin gadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.