Isa ga babban shafi
Amurka

Donald Trump ya far wa ‘yan jarida

Shugaban Amurka Donald Trump ya soki kafafen yada labarai da kakkausan harshe dangane da rahotannin da suke yayatawa na alakarsa da kasar Rasha da kuma shafa wa himmarsa ta dawo da martabar Amurka bakin fenti.

Donald Trump a yayin sa-in-sa da wani dan jarida.
Donald Trump a yayin sa-in-sa da wani dan jarida. REUTERS/Ben Brewer
Talla

Donald Trump ya bayyana hakan ne a yayin jawabi ga taron manema labarai da ya kira a Washington.

Trump ya kuma koda nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta samu a bangaren farfado da karsashin kasuwar hada-hadar hannun jarin kasar, da kuma kamen bakin haure da ba su da takardun izinin zama a Amurka.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin taron manema labaran tsawon mituna 76 Trump ya ce abin takaici ne ganin yadda  rashin gaskiyar kafafen yada labaran ya wuce kima.

Donald Trump ya kuma zargi kafafen yada labarai musamman na kasar da yi wa wasu ‘yan tsiraru aiki.

Wannan dai ba shi ba ne karon farko da Trump ke sukar 'yan jarida ko shiga sai-in-sa da su tun bayan da ya soma jan ragamar mulkin Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.