Isa ga babban shafi
Amurka

Mutane 2000 sun yi zanga-zanga a inda Trump ke ziyara

Mutane akalla 2,000 suka yi wata ‘yar kwarya-kwaryar zanga-zanga kusa da wani filin wasannin kwallon lambu na Shugaban Amurka Donald Trump a Florida.

Shugaban Amurka Donald Trump da Uwargidansa Melania
Shugaban Amurka Donald Trump da Uwargidansa Melania
Talla

Masu zanga zangar sun cigaba da la’antar matakai da kuma manufofin Trump, musamman matakin da ya dauka makonni biyu baya da ya kama aiki, na dokar haramtawa Musulmi shiga kasar.

Donald Trump da matarsa Melania Trump na halartan wani shaani ne a yankin a lokacin da aka yi wannan zanga-zanga.

Masu zanga-zangan sunyi ta munanan kalamai da matakan da Donald Trump ke dauka musamman na Koran baki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.