Isa ga babban shafi
MDD

Guterres ya bukaci Trump ya janye dokar hana shiga Amurka

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira ga gwamnatin Donald Trump ta gagaguta janye dokar haramtawa kasashe bakwai shiga Amurka domin hakan ba zai magance barazanar tsaron kasar ba.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres DR
Talla

A ranar Juma’a ne Trump ya sanya hannun kan dokar haramta shigar baki a Amurka na tsawon watanni 4, tare da haramtawa bayar da biza ga kasashen Iran da Iraqi da Libya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen

Guterres ya ce daukar matakin ba zai zama dalilin hana ‘Yan ta’adda shiga Amurka ba.

Sannan Sakatare Janar din na Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa manema labarai cewar matakan sun sabawa dokokin duniya tare da yin kira ga gwamnatin Trump ta sake tunani kan soke shirin tsugunar da baki ‘yan gudun hijira daga Syria.

Trump dai na son rage yawan ‘Yan gudun hijirar da gwamnatin Obama ta yi alkawali karba 100,000 zuwa 50,000 tae da barazanar rage yawan kudaden tallafin da ta ke ba Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.