Isa ga babban shafi
Amurka

An kalubalanci dokar hana baki shiga Amurka

Wasu Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a kasar Amurka sun shigar da kara kotu dan kalubalantar matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na hana baki da masu ziyara daga wasu kasashen Musulmi 7 zuwa kasar.

Masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin shugaba Donald Trump à birnin Washington.
Masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin shugaba Donald Trump à birnin Washington. REUTERS/Aaron P. Bernstein
Talla

Kungiyar American Civil Liberties Union da wasu takwarorin ta suka shigar da karar bayan an tsare wasu ‘yan kasar Iraqi biyu a filin jirgin saman JF Kennedy da ke New York daren juma’a.

Kungiyar ta bukaci sakin mutanen biyu da ta ce an tsare su ba bisa ka’ida ba.

Jaridar New York Times ta ce tun jiya juma’a jami’an tashar jiragen Amurka suka fara aiwatar da umurnin hana baki daga wadanan kasashe 7 da Trump ya bada umurni.

Kungiyar ta Civil Liberties ta ce daya daga cikin mutanen da aka tsare ya yi wa gwamnatin Amurka aiki na shekaru 10 a Iraqi, yayin da na biyun kuma ya isa kasar ne dan zuwa wajen matar sa wadda ke yi wa wani dan kwangila aiki, kuma dukkan su suna da izinin shiga Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.