Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya nada McMaster a matsayin mai bashi shawara kan tsaro

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya nada Janar H.R. McMaster a matsayin sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro dan maye gurbin Michael Flynn da ya sauka daga mukamin sa makon jiya.

Shugaba Donald Trump ya nada McMaster a matsayin sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro
Shugaba Donald Trump ya nada McMaster a matsayin sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Fadar shugaban kasar ta ce shugaba Trump ya bai wa sabon mai ba shi shawaran damar nada duk wadanda yake so ya yi aiki tare da su.

Tsohon mai bai wa Trump Shawara, Micheal Flynn, ya yi murabus ne sakamakon samunsa da alaka da gwamnatin Rasha da kuma boyewa Mataimakin shugaban kasar Amurka da hukumar FBI gaskiyar lamarin.

Mista Trump ya dau lokaci yana laluben maye gurbin Flynn, bayan wani sojin ruwan kasar Admiral Robert Harward ya ki amince da tayin shugaban.

Sabon jami’in na yanzu McMaster, ya yi kaurin suna wajen sukar yadda Amurka ta yi yakin Vietnam da kuma lokacin da ya jagoranci yakin Iraqi a shekarar 2005.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.