Isa ga babban shafi
Iraqi

Sojojin Iraqi sun kaddamar da yakin Kwato Mosul

Gwamnatinm Iraqi ta ce dakarunta sun kaddamar da farmakin karshe na kawato Mosul daga hannu mayakan ISIL irinsa mafi girma da zai iya salwantar da rayuka da dama.

Dakarun Iraqi da ke kokarin gani sun kakkabe IS a Mosul
Dakarun Iraqi da ke kokarin gani sun kakkabe IS a Mosul REUTERS/Ahmed Saad
Talla

Daga kaddamar da farmakin yau lahadi zuwa yanzu an kwato kauyuka biyu daga mayakan a kudancin birnin Mosul.

Tun a jiya Assabar, Ma’aikatar tsaron kasar ta ce jiragen yakin sama na ta watsa wasu takardu da ke gargadin mazauna yammacin birnin Mosul su kauracewa gwabzawar da za a yi da mayakan IS.

Rahotanni sun ce tuni dakarun gwamnati suka yiwa mayakan kawanya a garin, inda aka kiyasta akwai fararen hula sama da dubu 650.

Takardun da aka raba sun ce tuni dakarun gwamnati suka fara danna kai cikin birnin na Mosul domin fatattakar mayakan na IS.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.