Isa ga babban shafi
Iraqi

Mutane 68,000 sun rasa muhallansu a Mosul

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 68,000 ne suka tsere daga gidajensu, bayan kaddamar da yaki kan mayakan IS a birnin Mosul da rundunar sojin Iraqi ta yi.

Wasu da yakin Mosul ya raba da muhallansu
Wasu da yakin Mosul ya raba da muhallansu REUTERS/Azad Lashkari
Talla

Rahoton Majalisar, ya kuma ce har yanzu, akwai fararen hula sama da miliyan daya da yaki ya ritsa da su cikin birnin na Mosul, wadanda ke bukatar agaji.

Ofishin samar da jinkai na majalisar Dinkin Duniya OCHA, ya ce yanzu haka yana fuskantar kalubalen lura da dubban ‘yan gudun hijira, sakamakon yawansu da ke karuwa, tun bayan kaddamar da farmakin kan birnin Mosul.

To sai dai kuma wani binciken ma’aikatar harkokin waje ta Iraqi, ya ce yawan mutanen da yakin ya raba da muhallansu a birnin, ya gaza kaiwa yawan da aka zata da fari.

A watannin baya, Majalisar Dinkin Duniya, ta yi hasashen akalla fararen hula 200,000 ne zasu rasa muhallansu, idan har rundunar sojin Iraqi da kawayenta suka kaddamar da farmaki kan Mayakan IS a birnin na Mosul.

A halin da ake ciki, duk da gargadi da sojin Iraqi ke aikewa fararen hula, na su fice daga birnin, kakakin wata hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norway, Becky Bakr Abdulla, ya ce kawo yanzu babu wasu hanyoyi da aka samarwa mutanen, domin samun damar ficewa daga birnin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, sansanin da ke dauke da wadanda suka rasa muhallansu a Mosul, na cigaba da tumbatsa, tare da hasashen yawansu daga 68,000 zai karu zuwa 500,000 a watan Disamba mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.