ISIL za ta ci gaba da fafutuka don rike birnin Mosul
Shugaban Kungiyar ISIL Abubakar al-Baghdadi ya bukaci mayakan sa dake Mosul da kar su bada kai bori ya hau a fafatawar da suke wajen ci gaba da iko da garin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya aika ta intanet, inda yake shaida musu cewar ci gaba da tirjiya wajen kare garin shine mafi alkhairi a gare su.
Baghdadi ya gargadi mayakan da su kare kasar su wajen yakar mayakan dake neman raba su da garin.
Babban birnin Mosul wadda shine gari na biyu mafi girma a kasar Iraki ya fada hannun kungiyar ISIL shekaru biyu da suka gabata kafin yanzu gwamnati kasar ta yunkuro da shirin sake karbe birnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu