Mutane 213 ne suka mutu a harin ta'addanci a Bagadaza na Iraki
Jimi'llan mutane 213 aka karas da sun gamu da ajalinsu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai birnin Bagadaza na kasar Iraqi ranar lahadi, wanda kungiyar IS ke ikirarin ita ta kai shi.
Wallafawa ranar:
Jami’an Gwamnatin kasar suka gabatar da sabbin alkaluman mamatan a yau littini a birnin Bagadaza.
Harin na kunar bakin wake, cikin wata mota da aka shake ta da bama-bamai an kaishi ne a wani yanki da jama’a ke taruwa, da gine-gine da shaguna masu yawa.
Jimi'llan mutane 200 suka jikkata kamar yadda jami'an tsaro da majiyoyi a asibiti suka shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu