Dakarun Iraki sun kwace birnin Nimrud daga hannun ISIL
Birnin Nimrud mai dimbin tarihi ya subuce daga hannun mayakan ISIL bayan da dakarun sojin Iraqi suka yi nasarar kwace garin daga hannun mayakan a farmakin da ake ci gaba don karbe ikon birnin Mosul.
Wallafawa ranar:
Birgediya Janar Saad Ibrahim, kwamanadn runduna ta 9 ya sanar da nasarar, inda ya ke cewa tuni suka karbe kauyukan Al Nomaniyah da Al Nimrud.
Nimrud na daya daga cikin tsofin garuruwan Gabas ta Tsakiya da aka kafa tun a karni na 13 kafin zuwan Annabi Isa Alaihis Salam, kuma ya taba zama babban birnin Daular Syria na wancan lokaci inda Sarakunan kasar suka gina manyan gine gine.
Shekaru biyu da suka wuce ne Kungiyar ISIL ta karbe ikon birnin .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu