Isa ga babban shafi
Faransa

Wanda ya kai hari gidan tarihin Louvre da adda yaki magana

Masu Gudanar da bincike a Faransa sun fara yiwa mutumin da aka harba a gidan aje kayan tarihin Paris tambayoyi amma kuma yaki bada amsa, kamar yadda majiyar shari’a ta sanar da manema labarai.

Talla

Bayanai sun ce masu gabatar da karar sun bukaci yiwa wanda ake zargin yunkurin kaiwa sojin dake gadin tarihin hari da wuka tambayoyi ne bayan ganin an fara samun lafiya sakamakon harbin da aka masa.

An dai harbi Abdallah El-Hamahmy, Dan kasar Masar a ciki ne ranar juma’ar da ta gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.