Isa ga babban shafi
Faransa

An harbe maharin gidan tarihin Louvre a Paris

Wani jami’in sojin Faransa ya harbe wani mutum dauke da wuka bayan ya yi yukurin kai hari a gidan ajiye kayayyakin tarihi na Louvre da ke birnin Paris na Faransa.

Jami'an tsaron Faransa na kwashe masu yawan bude ido a gidan tarihin Louvre na Paris bayan wani yunkurin harin ta'addanci a yau Jumma'a
Jami'an tsaron Faransa na kwashe masu yawan bude ido a gidan tarihin Louvre na Paris bayan wani yunkurin harin ta'addanci a yau Jumma'a ALAIN JOCARD / AFP
Talla

Rahotanni sun ce, an ji mutumin na fadin Allahu Akbar a yayin yunkurin harin, amma jami’in sojin ya dirka masa bindiga a ciki.

Firamininistan kasar Bernard Cazeuneuve ya bayyana harin tamkar na ta’addanci, yayin da kuma aka shawarci baki da ke ziyara a gidan tarihin da su zauna a kasa saboda kare kansu.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, maharin na dauke da jakunkuna guda biyu da ake ratayawa a baya, amma babu bama-bamai a cikinsu.

Kimanin baki 250 ne ke ziyara a gidan tarihin na Louvre a lokacin da wannan lamarin ya faru a yau Jumma’a, yayin da ake ci gaba da kwashe su daya bayan daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.