Faransa za ta kara kaimin yakar ‘Yan ta’adda a Sahel
Firaministan Faransa Bernard Cazeneuve da ke ziyara a kasashen Sahel ya ce Faransa za ta kara yawan kasafin tsaro ga sojojinta da ke yaki da ta’addanci a yankin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Bernard Cazeneuve ya fadi haka ne a N’Djamena, a ziyarar farko da ya kai a yankin Sahel a matsayin Firaminsitan Faransa.
Firaministan ya ce za su ci gaba daukar matakan da za su dore ga tabbatar da tsaron Faransa.
Sannan ya ce Faransa za ta kasance a cikin shirin yaki a kodayaushe kuma a ko wane yanki har sai an kakkabe ‘Yan ta’adda.
Cazeneuve dai na amfani da ziyara ne domin sake jaddada goyan bayan Faransa a yaki da ta’adanci tare da sake duba sabbin hanyoyin karfafa hulda da kasashen Sahel ta fuskar tsaro.
Faransa na da dakaru kimanin 4,000 a kasashen Mouritania da Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu