Isa ga babban shafi
Faransa

Benoit Hamon ya lashe zaben fidda gwani

Magoya bayan Jam’iyyar Socialists mai mulkin Faransa sun zabi Benoit Hamon a matsayin dan takarar zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Mayu mai zuwa.

Benoît Hamon zai tsaya takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Socialist.
Benoît Hamon zai tsaya takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Socialist. REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Hamon ya kada tsohon Firaminista Manuel Valls a zaben fidda gwani zagaye na biyu da aka yi a karshen mako.

Tsohon ministan ilimi Benoit Hamon ya samu kashi sama da 58 na kuri’un da aka kada wajen kayar da Manuel Valls, tsohon Firaministan da aka dade ana hasashen cewar zai samu nasara.

Wannan nasara dai ta bai wa masu sa ido kan harkokin siyasar Faransa mamaki, ganin yadda tsohon ministan, wanda da ne ga wani ma’aikacin tashar jiragen ruwa ya bai wa marada kunya.

Hamon ya shaidawa magoya bayan sa cewar, Faransa na bukatar tafiya da zamani wajen kawo sauyin da zai taimakawa jama’a ba wasu ‘yan kadan ba.

Yanzu zai kara da Francois Fillon da Marine Le Pen da Emmanuel Macron a zaben gama gari da za’ayi a watan Mayu dan samun wanda zai maye gurbin shugaba Francois Hollande.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.