Isa ga babban shafi
Faransa

Wani bincike yace Kashi 32 cikin 100 zasu kauracewa zaben Faransa

Mako uku a gudanar da zaben shugaban kasar Faransa, wani binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar ya nuna cewa kashi 32 cikin dari na masu kada kuri’a zasu kauracewa zaben saboda rashin gamsuwa da yakin neman zaben ‘Yan takara.

Tutar kasar Faransa mai dauke da hoton wani zai kada kuri'ar zaben shugaban kasa
Tutar kasar Faransa mai dauke da hoton wani zai kada kuri'ar zaben shugaban kasa Montaje RFI
Talla

Binciken da wani kamfanin na IPOF ya gudanar ya nuna cewa kashi daya cikin uku na al’ummar kasar Faransa zasu kauracewa zagayen farko na zaben shugaban kasa da za’a gudanar.

Jaridar Le monde daily tace hakan zai faru ne saboda wasu ‘yan kasar basu gamsu da yakin neman zaben ‘Yan takara ba saboda rashin cika alkawali.

A zaben bana da za’a gudanar a Faransa, ana hasashen shugaba Sarkozy da Hollande na Jam’iyyar gurguzu ne zasu taka rawa a zagayen farko cikin ‘Yan takara 10 masu neman kujerar shugabancin kasar.

Hollande wanda ke samun goyon bayan Faransawa, ya fuskanci cikas bayan bulluwar dan takara Jean-Luc Melenchon, amma har yanzu yana ci gaba da sukar Sarkozy.

A jiya Lahadi hollande ya soki gwamnatin Sarkozy wajen gazawa ga samar da aikin yi ga matasa.

Sai dai kuma  Nicolas Sarkozy, ya bayyana sabbin shirye shiryen tallafawa matasa, domin samun goyan bayan su a zaben shuagaban kasa mai zuwa.

A lokacin da shugaban ke jawabi ga wani taron matasa 7,000 a karshen mako, Sarkozy ya yi alkawarin kafa Bankin matasa, wanda zai basu rance ba tare da ruwa mai yawa ba, domin gudanar da sana’oi, tare da ribanya yawan matasan da zasu yiwa kasa hidima,

Shugaban ya bukaci kamfanonin da ke da ma’aikata sama da 250, ware kashi biyar na gurabe ga matasan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.