Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya lashe wani zaben jin ra’ayin Jama’a a Faransa

A karon farko Wani zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Faransa ya nuna Shugaba Nicolas Sakozy ne akan gaban abokin hamayyarsa Francois Hollande a zaben zagaye na farko na shugaban kasa, kodayake zaben ya nuna Hollande ne zai lashe zagaye na biyu da za’a gudanar a watan Mayu.

Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy
Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Charles Platiau
Talla

Zaben ra’ayin jama’ar da aka gudanar ya nuna Sarkozy ya samu kashi 28.5 na yawan kuri’u a zaben zagayen farko amma Hollande ya samu yawan kuri’u kashi 27.

Sakamakon zaben ya nuna Hollande ne zai lashe zaben zagaye na biyu da yawan kuri’u 54.5 inda Sarkozy zai samu kuri’u kashi 45.5.

Zaben kasar Faransa a bana hamayya ce tsakanin Sarkozy wanda ya yi alkawalin magance kwararar ‘yan gudun Hijira tare da inganta tattalin arzikin Faransa, da kuma Abokin Hamayyarsa Hollande wanda ya sha alwashin inganta Haraji da tsarin kashe kudaden gwamnati.

Shugaba Sarkozy dai yana neman wa’adi na biyu ne duk da kasancewar shi shugaba wanda ba shi da yawan magoya baya a sabuwar Faransa inda yawancin al’ummar kasar basu gamsu da tsarin gwamnatin shi wajen inganta tattalin arziki.

Zaben jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a baya sun nuna Sarkozy zai sha kaye a zaben bana, duk da ruwa da tsaki da shugaban ke yi wajen yaki da matsalar tattalin arzikin da ya addabi wasu kasashen Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.